Labarai
AA Zaura ya bayarda tallafin miliyan 200 ga ɗalibai dubu goma 10,000 ƴan asalin Jihar Kano da suke karatu a Jami’o’i da kwalejoji daban daban.

Mai neman takarar Gwamna a Jihar Kano, wato Abdulsalam Abdulkarim wanda aka fi sani da AA Zaura, ya bayarda tallafin naira miliyan 200 ga adadin ɗalibai 10,000 ƴan asalin Jihar Kano da suke karatu a Jami’o’i da kwaleji daban-daban dake faɗin Nigeria.
AA Zaura ya bayyana cewa babban abin da yake sanya al’umma ta cigaba shine ilimi, kuma matasa suna da buƙatar tallafi a ɓangaren, wannan dalilin ne ma ya sanya ya ga dacewar ya tallafa musu da miliyan 200.
Masu buƙata za su iya ziyartar wannan shafin https://aazaura.org.ng/education-support-fund/ domin gwada tasu sa’ar.