
Soyayya ta kullu tsakanin jaruman Kannywood biyu Ummi Rahab da kuma Lilin Baba.
jarumar ce ta wallafa hakan a shafukan ta na sada zumunta na Instagram da kuma TikTok.
Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin datake taya Lilin murnar zagayowar ranar haihuwar shi,Wanda hakan ya jawo kace nace sosai a inda wasu suke ganin hakan kamar tayi ne domin neman gindin zama a wajen Ogan nata na yanzu Lilin Baba.
Wasu kuma na ganin tabbas Soyayyar ce ta kullu a tsakanin jaruman amma kawai soyayya ce da kauna ba wai Soyayyar yin aure ba.
Jarumar dai tun bayan barin ta daga gurin jarumi Adam Zango ta koma izuwa jarumi kuma mawaki a Kannywood Lilin Baba.
Ga wasu hotunan abun da jarumar ta wallafa a shafin ta na Instagram: