Labaran Siyasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnatinsa zata cigaba da ƙoƙarin bijoro da shirye-shiryen tallafawa talakawa duk da matsalar tsaron da ake fama a Nigeria.

  Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnatinsa zata cigaba da ƙoƙarin bijoro da shirye-shiryen tallafawa talakawa duk da matsalar tsaron da ake fama a Nigeria.

 

 

Buhari ya bayyana haka ne a yau Asabar cikin saƙon barka da sabuwar shekara da ya aike ga ƴan Nigeria.

 

 

 

Ya bayyana cewa, “yana ƙunshe cikin tarihi yadda Gwamnatinsa ta zuba jari domin samar da kayan yaƙi ga dakarun ƙasar nan ta yadda za’a magance matsalar tsaro a Nigeria.

 

 

 

Ya kuma ƙara da cewa, duk da irin ƙalubalen da aka fuskanta a shekarar 2021, ta fanni guda an samu nasarar kammala waɗansu muhimman ayyuka daban-daban.

 

 

 

A ƙarshe, Buhari ya umarci ƴan Nigeria akan su ƙara sanya lumana a ransu, tare da ƙarfafawa Gwamnati da jami’an tsaro gwiwa wajen ganin an shawo kan matsalar tsaro da tattalin arziƙi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!