Labaran Duniya

Ɗan takarar mataimakin gwamna na NNPP ya ajiye takara tare da fice wa daga jam’iyyar

Ɗan takarar mataimakin gwamna na NNPP ya ajiye takara tare da fice wa daga jam’iyyar

Mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, a jihar Neja, John Bahago, ya fice daga jam’iyyar tare da ajiye takarar sa a matsayin mataimakin na gwamna.

 

Bahago, wanda tsohon dan majalisar dokokin jihar Neja ne ya bayyana hakan a wata wasika da ya aike wa shugaban gundumar Guni, mai kwanan wata 14 ga Disamba, 2022.

 

A cewar wasikar, wacce kuma aka aike da kwafinta zuwa ga shugaban karamar hukumar Munya na jam’iyyar da kuma shugabannin jaha da na kasa, Bahago ya gode wa jam’iyyar bisa goyon bayan da ta ba dan takarar gwamna Yahaya Ibrahim na jam’iyyar.

 

Ko da yake ba a bayyana dalilin da ya sa ya dauki matakin ba, jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa reshen jam’iyyar na jihar da Mista Sokodeke sun yi ta fafatawa a kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa jam’iyyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!