Ɗan A daidaita Sahu a jihar Kano, ya mayar da kusan Naira Miliyan 15 da aka manta a babur ɗin sa

‘Dan Sahu ya Maida Miliyoyin Ku’di daya Tsinta
Wani matashi dake tuka Babur din Adaidaita Sahun mai suna Auwalu Salisu Wanda aka fi Sani da Na Baba dake bayan tashar Yan Kaba, ya dawo da wasu kudi Mallakin Alhaji Ibrahim Barka Daga kasar Chadi da aka manta a babur dinsa ranar Alhamis din data gabata.

Play ▶️
Kudin akwai Saifa Milyan 10 da Dubu 130 sai kuma sama da Naira Milyan 2 biyo bayan jin sanarwar cigiyar kudin a tashar Arewa Radio 93.1.
Watch the video
Daga karshe an bashi tukuichin tsintuwa har Naira Dubu ‘Dari 400.
Rabiu Biyora mai amfani da shafin Facebook ya bayyana a shafin sa kamar haka:
DAN ALBARKA…..
An manta kudaden da yawansu ya haura Naira miliyan goma sha biyu a cikin Adaidaita sahun da yake tukawa, bayan yaga kudin sai ya koma inda ya sauke fasinjan ko zai ganshi amma bai tarar dashi ba, sai ya kai kudaden wajen mahaifiyarsa ya gaya mata cewa manta kudaden akayi a Adaidaita dinsa, nan take mahaifiyarsa tace yaje ya gayawa Mahaifinsa inda nan take Mahaifin yaron yace su koma su sake dubawa ko zaa ga mai kudin, da baa gani ba sai suka ajiye kudin a gida, basu taba ko sisi ba duk da cewa jiya da kyar suka samu garin kwakin da suka ci a gidan nasu kamar yadda Mahaifin yaron ya fada…
Sunji ana cigiya a gidan Rediyon Arewa dake kano, inda nan da nan suka dauki lambar wayar da aka bayar suka kira …
A takaice dai yaron da iyayensa sun mayarwa da mutumin da ya manta kudaden abunsa, inda shi kuma ya basu kyautar Naira dubu dari hudu…
Wannan yaro ya kyauta…..