Labaran Duniya

Ƴan ta’addan ISWAP 104 sun miƙa wuya tare da zubar da makamansu ga Sojoji a Jihar Borno.

Aƙalla mayaƙan ISWAP 104 ne suka miƙa wuya tare da iyalansu ga Jami’an Sojin Nigeria masu bataliya a ƙaramar hukumar Damboa dake Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa, a jerin waɗanda suka miƙa wuyan tare da zubar da makamansu sun haɗa da matasa tare da dattijai da suka daɗe suna ta’addanci ƙarƙashin ƙungiyar ta ISWAP.

A watannin baya ma an samu da yawa daga cikin mayaƙan da suka miƙa wuya sakamakon matsa korar da Jami’an Sojin Nigeria su ka yi musu a yankunan nasu dake Arewa maso gabashin Nigeria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!