Tsaro

Ƴan bindiga sun kuma sako mutane 97 da sukayi garkuwa da su tsawon watanni 3.

Aƙalla mutane 97 ne suka kuɓuta daga hannun ƴan bindiga bayan shafe tsawon watanni 3 a garƙame.

Hukumar ƴan sandan Jihar Zamfara ta bayyana cewa sune suka kuɓutar da mutanen. Yayinda a gefe guda kuma wasu kafofin yaɗa Labarai suka tabbatar da cewa ƴan bindigar ne suka saki mutanen da kansu.

Kwamishinan ƴan Sanda na Jihar Zamfara, mai suna Ayuba Elkanna yayi jawabin cewa kuɓutar mutanen yana da babbar alaƙa da matsin lamba da ƴan bindigar suka fuskanta a baya-bayan nan daga Jami’an tsaron Nigeria, musamman a yankunan Shinkafi, Zurmi da kuma karamar hukumar Birnin Magaji dake Jihar Zamfara.

Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa, mutanen da aka sallama ɗin sun shafe aƙalla watanni 3 a garƙame.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!