Uncategorized
Ƴan bindiga sun kashe mutane 20 tare da ƙone motoci da gidaje a ƙauyukan Giwa, Jihar Kaduna.
Hukumar Sojoji da ƴan Sanda a Jihar Ƙaduna ta ruwaito yadda ƴan Bindiga suka kashe mutane 20 bayan sun kai hari a ƙauyukan ƙaramar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.
Kwamishin tsaro da al’amuran cikin na Jihar Kaduna wato, Samuel Aruwan ya tabbatar da cewa harin na ƴan Bindigar ya shafi ƙauyuka da dama kamar; Kauran Fawa, Marke da Riheya duk a cikin ƙaramar hukumar ta Giwa.
Ya kuma ƙara da cewa, ” ƴan bindigar sun ƙone gidade, amfanin gona tare da manya da ƙananan motoci.
Gwamna El-Rufai ya samu rahoton faruwar al’amarin cikin takaici, kuma Gwamnan yayi addu’a tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda al’amarin ya shafa.
Www.labarai.com.ng