Uncategorized
Ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa CAN, ta bayyana rashin amincewarta akan sauya ranakun aiki zuwa kwanaki huɗu a Jihar Kaduna.
Ƙungiyar Kiristici ta ƙasa CAN reshen Jihar Kaduna ta hau teburin naƙi dangane da kuɗirin Gwamna El-Rufai na mayarda ranakun aiki kwana huɗu, tare da zargin cewa akwai boyayyen shiri a lamarin.
A ranar Litinin ne Gwamnan ya bayyana ƙudirin Gwamnatinsa cewa an cire ranar Juma’a daga cikin ranakun aiki a faɗin Jihar, kuɗirin da zai fara wanzuwa a gobe 1 ga watan Disamba 2021.
Yayin sharhi dangane da lamarin, Shugaban ƙungiyar ta Kiristoci CAN mai suna John Joseph-Hayab yayi jaje tare da yin Allah-wadai bisa ga irin ƙudure-ƙuduren da Gwamnan yake bijirowa dasu a Jihar.
Mista Hayab, yayi kira ga ɗaukacin ma’aikata a faɗin Jihar akan kar su fara murna har sai sun tabbatar babu wata ɓoyayyen manufa a lamarin.
Www.labarai.com.ng