Labaran Duniya

Ƙungiyar dattawan yankin IGBO sun roƙi Buhari akan ya bayarda belin Nnamdi Kanu.

Ƙungiyar dattawa ta yankin IGBO sun roƙi Shugaba Buhari akan ya saki Nnamdi Kanu, a cewar su cigaba da kulle Kanu yana ƙara haddasa fituntunu a yankunan na su.

Sun aika wannan roƙo ne cikin wata wasiƙa da wasu daga cikin shuwagabannin suka sanya hannu daga yankin na kudu maso gabashin Nigeria.

Sun bayyana ƙarara cewa cigaba da kulle Kanu ba shi da amfani ga mazauna yankin na IGBO.

Sun ƙara da cewa, Idan har gwamnati tana fatan zaman lafiya ya wanzu, kuma a cigaba da harkokin kasuwanci, toh ya zama wajibi a bayar da belin Mazi Nnamdi Kanu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!